Mr. Li wanda ya bayyana hakan yayin taron 'yan kasuwa na Davos wanda ya gudana a Arewa maso Gabashin kasar Sin, ya bayyanawa mahalarta taron cewa rage darajar kudin Yuan domin bunkasa fidda kayayyaki, ba manufa ba ce da ta dace da tsarin gyaran fuskar tattalin arziki da Sin ke aiwatarwa.
Daga nan sai ya jaddada cewa kasar Sin ba ta fatan ci gaba da rage darajar kudin na Yuan. (Saminu Alhassan)