A jiya ne 'yan kasar Iran daga sassa daban daban na kasar suka yi wata zanga-zangar nuna adawa ga kasar Amurka, domin tunawa da cika shekaru 36 da mamaye ofishin jakadancin kasar Amurka dake Iran da daliban kasar Iran suka yi inda suka yi garkuwa da wasu Amurkawa.
Iraniyawa a sassa daban daban na kasar, sun gudanar da gagarumin zanga-zanga. A birnin Tehran, babban birnin kasar Iran, mazauna birnin sun yi tattaki daga jami'ar Tehran zuwa tsohon ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar.
A ranar 4 ga watan Nuwamba na shekarar 1979 ne, dalibai masu tsattsauran ra'ayi suka kutsa kai cikin ofishin jakadancin kasar Amurka, inda suka yi garkuwa da jami'an ofishin jakadancin kasar Amurka har na tsawon kwanaki 444, hakan ya sa huldar dake tsakanin kasashen Iran da Amurka ta raunana. A ranar 7 ga watan Afrilu na shekarar 1980, an yanke huldar dake tsakanin kasashen biyu. Daga bisani, kasar Amurka ta kakkaba wa kasar Iran takunkumi. Iraniyawa dai na kallon kasar Amurka a matsayin abokiyar gabar su.
A ranar 14 ga watan Yuli na wannan shekara, kasar Iran da kasashen nan 6 da batun nukiliyar Iran ya shafa suka cimma yarjejeniya game da shirin nukiliyar kasar ta Iran, a matsayin wani mataki na soke takunkumin da kasashen yamma suka kakaba wa kasar Iran. A ranar 7 ga watan Oktoba, jagoran addinin kasar ta Iran Ayatollah Ali Khameni ya hana gwamnatin kasar Iran yin shawarwari tare da kasar Amurka kan harkokin da suka shafi bangarorin biyu har ma da na bangarori dadama.(Lami)