Madam Marzieh Afkhan za ta kama aiki a matsayin jakadan kasar Iran a kasar Malaisiya a karshen watan Nuwamba.
Madam Afkhan, dake jagorantar cibiyar kula da diplomasiyyar jama'a da yada labarai a ma'aikatar harkokin wajen kasar a wadannan shekaru na baya baya, ta kasance mace ta farko kakakin ma'aikatar tun daga watan Satumban shekarar 2013, ranar da Hassan Rohani ya kama aiki.
Mace jakada ta baya bayan 'yar kasar Iran, ita ce Mehranghiz Dolatshahi, wanda ta wakilci Teheran a kasar Danrmark a tsawon shekaru uku har zuwa lokacin juyin juya halin musulunci a shekarar 1979, a cewar kamfanin dillancin labarai na ISNA. (Maman Ada)