in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bahrain ta sanar da yanke huldar diplomasiyya dake tsakaninta da Iran
2016-01-04 20:25:37 cri

A yau ne kasar Bahrain ta sanar da yanke huldar diplomasiyya dake tsakaninta da kasar Iran, inda ta bukaci ma'aikatan diplomasiyya na Iran da su bar kasar cikin sa'o'i 48. Bugu da kari, gwamnatin Bahrain ta yanke shawarar rufe ofishin jakadancinta da ke kasar Iran kana ta janye ma'aikatan diplomasiyyarta daga Iran din.

Har wa yau kuma, a yau ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Ansari ya ce, matakain da kasar Saudiya ta dauka na yanke huldar diplomasiyya da Iran, babban kurkure ne da ka iya dagula al'amura.(Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China