Ministan harkokin wajen Saudiyya Adel al-Jubeir ya bayyana cewa an sanar da kwamitin tsaro na MDD game da harin da aka kai wa ofishin jakadancin Saudiyya dake Iran a ranar Asabar, inda ya kara da cewa dukkan jami'an dipolmasiyyar Saudiyya sun samu damar isa Dubai na hadaddiyyar daular kasashen labarabawa lami lafiya.
Haka kuma ya zargi hukumomin Iran da kasa daukar matakai domin hana kai wa ofishin jakadancin dake Teheran da kuma karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Mashhad na Iran hare hare.
A ranar Asabar, wasu masu zanga zanga 'yan kasar Iran cikin bacin rai sun afkawa ofishin jakadancin Saudiyya bayan da kasar ta aiwatar da hukuncin kisa kan mutane 47 da take zarginsu da ta'addanci, daga cikinsu akwai dan Shi'a nan Nimr Al-Nimr, mamba na kungiyar 'yan shi'a ta Saudiyya. (Maman Ada)