Majalisar dokokin Iran ta amince da shirin daukar matakai game da batun nukiliyar kasar
Bisa labarin da gidan talibijin na kasar Iran ya bayar da safiyar yau din nan, a yayin wani taron da aka gudanar, majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar amincewa da "shirin daukar matakai daga dukkan fannoni" game da batun nukiliyar kasar ta Iran.
A ranar 14 ga watan Yulin wannan shekara ne, aka kulla wannan "shiri na daukar matakai daga dukkan fannoni" game da batun nukiliyar kasar a birnin Vienna na kasar Austria a tsakanin kasar Iran da manyan kasashe 6, wato Amurka, Rasha, Faransa, Ingila, Jamus da kasar Sin. (Sanusi Chen)