A wannan rana kuma, ministan dake kula da harkokin Arabiya da Afirka na ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir Abdollahian ya kira taron gaggawa tare da jakadan kasar Saudi Arabiya dake kasar Iran da kuma nuna adawa kan kashe dan Shi'ar mai suna Sheikh Nimr Baqr al-Nimr da kasar Saudi Arabiya ta yi.
Kaza lika, shugaban kwamitin dake kula da harkokin tsaro da diflomasiyya na majalisar dokokin kasar Iran Alaeddin Boroujerdi ya yi kira ga ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran da ta dauki matakai wajen rage adadin wakilan kasar Saudi Arabiya dake kasar yadda ya kamata, da kuma rage matsayin dangantakar diflomasiyyar dake tsakanin kasashen biyu.
A babban garin Shi'a dake arewa maso gabashin kasa ta Iran, Mashhad, mazauna wurin da dama sun taru a gaban karamin ofishin jakadancin kasar Saudi Arabiya dake wurin a daren ranar 2 ga wata, domin nuna adawa da kashe Sheikh Nimr Baqr al-Nimr da gwamnatin kasar ta yi kwanan baya.
Kana a ran 2 ga wata, ma'aikatar harkokin wajen kasar Saudi Arabiya ta kuma nuna bacin ranta kan jakadan kasar Iran dake kasar bisa zargin kasar Iran da tsoma baki cikin harkokin gidan kasarta, ta kuma yi suka da kakkausar murya game da yadda kasar Iran ta rura wutar kiyaya kan kasar bisa cewar ta kashe wani dan Shi'a, wanda ya aikata laifin ta'addanci a kasar Saudi Arabiya.
Kaza kila, kasar Saudi Arabiya ta kuma yi kira ga gwamnatin kasar Iran da ta kiyaye tsaron wakilan kasar dake kasar Iran bisa dokokin kasa da kasa da abin ya shafa yadda ya kamata, domin kare lafiyarsu. (Maryam)