Sin da Amurka da Iran sun cimma matsaya kan sake fasalin na'urorin sarrafa nukiliya da ke Arak
Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar Sin ta bayyana a cikin wata sanarwa jiya cewa, shugaban hukumar Xu Dazhe da ministan makamashi na kasar Amurka Ernest Moniz tare kuma da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar Iran Ali Akabar Salehi a kwanan baya a madadin kasashen uku suka cimma yarjejeniya game da sake fasalin na'urorin sarrafa nukiliya da ke birnin Arak na Iran bisa shirin JCPOA.
Sanarwar ta nuna cewa, hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar Sin da kuma ma'aikatar makamashin nukiliya ta kasar Amurka a madadin kasashe shida da batun nukiliya na kasar Iran ya shafa, za su hada gwiwa da bangaren Iran a kokarin sake fasalin na'urorin sarrafa nukiliya da ke Arak. Sanarwar da aka cimma ta bayyana aniyyar kasashen uku na sake fasalin na'urorin, matakin da ake fatan zai taimaka wajen aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka cimma a kwanakin baya yadda ya kamata. (Lubabatu)