Gidan telebijin na kasar Iran ya bayyana cewa, Salehi ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da wakilan kamfanin dillancin labaru na Kyodo na kasar Japan a wannan rana. Salehi ya bayyana cewa, Iran ta fara aikin cire na'urorin tace sinadari da ba a bukatansu, kuma ana sa ran kammala wannan aiki a cikin watanni biyu.
Salehi ya kara da cewa, cire na'urorin shi ne matakin farko na aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar kasar ta Iran, kasar Iran tana bukatar karin lokaci kafin ta kammala sauran ayyukan da aka tsara a cikin yarjejeniyar. Ya kuma jaddada cewa, bisa yarjejeniyar da aka cimma, kasar Iran tana iya barin wasu daga cikin na'urorin tace sinadaran da ke Natanz da Fordo don biyan wasu bukatunta. (Zainab)