in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Babu wani yanki dake karkashin mallakar Boko Haram
2015-12-27 14:21:43 cri
Wani jami'in kasar Najeriya ya shedawa manema labaru a jiya Asabar 26 ga wata cewa, sojojin kasar da aka jibge a arewa maso gabashin kasar, sun maido da duk yankunan da Boko Haram ta kwace.

Shugaban hukumar kula da halin ko ta kwana ta kasar (NEMA), mista Sani Sidi ya shedawa manema labaru a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin kasar cewa, an cimma nasara wajen yaki da Boko Haram, saboda haka, a cewarsa, dukkanin yankuna na karkashin ikon gwamnatin kasar.

Dadin dadawa, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayyana a Juma'a 25 ga wata cewa, yanzu ana kokarin yin kira ga mambobin Boko Haram da su ajiye makamai, su rungumi zaman lafiya a sauran yankunan kasar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China