Jaridar Vanguard na kasar ta ruwaito tun da farko ta cewar, mutane 100 ne hadarin ya rutsa da su a gobarar da ta tashi a gidan mai sakamakon fashewar tukwanen gas a wajen.
Sai dai kuma wani jami'in Red Cross wanda ya nemi a sakaya sunan shi ya ce wadanda suka mutu a gobarar nan take mutane 6 ne.
Haka shi ma kwamishinan 'yan sandan jihar Hosea Karma ya tabbatar da mutane 6 ne suka mutu, wadansu 6 kuma suka ji rauni.
A cewar ofishin kashe gobara na jihar, fashewar ta auku ne a gidan man Inter Corp wanda ya kawo mummunan tashin gobara. Wadanda tsautsayin ya rutsa da su 'yan gari ne da suka zo cika tukwanen gas din su da kuma masu wucewa a hanya.
Emeka Offor wani mazaunin wajen ya shaida ma Xinhua cewa gidaje da dama sun kone, sannan motoci fiye da 60 da Babura fiye da 50 duk sun kone a wannan wutan, baya ga mutane 20 da suka jikkata wanda saurin agajin da 'yan kwana kwana suka kawo ne ya takaita wutan.
Jami'in na Red Cross ya ce wadanda suka mutu an kai su dakin ajiye gawawwaki a asibitin garin, sannan wadanda suka jikkata aka kai su asibiti daban daban a cikin garin.
Kwamishin Karma ya ce babu ma'aikaci ko daya na wannan gidan man da ya mutu a gobarar. (Fatimah Jibril)