151128murtala.m4a
|
Bayan tsawon lokaci da jam'iyyar APC ta dauka tana tattaunawa, a jiya Jumma'a ta mika sunan Yahaya Bello a matsayin sabon dan takararta na gwamnan jihar Kogi a Najeriya.
Bello ya maye gurbin marigayi Yarima Abubakar Audu ne, wanda ya rasu a makon da ya gabata bayan yana kan gaba a zaben da ratar kuri'u dubu 41.
Haka kuma bincike ya nuna cewa har yanzu Honarabul James Abiodun Faleke shi ne a matsayin mataimakin dan takarar.
Babban dan marigayi dan takarar, Mohammed Audu da ake so ya maye gurbin mahaifinsa, jam'iyyar ta ajiye shi gefe ne, don gudun kada tsayar da shi ya jawo mata nakasu wajen kasa cin zaben.
Sai dai jama'ar yankin Kogi ta yamma sun yi ta jan hankalin Falake kan kada ya amince da tsayar da Bello a matsayin dan takarar da jam'iyyar ta yi.
Bincike ya nuna cewa shugabannin jam'iyyar APC tare da goyon bayan wasu daga cikin manyan mukarraban gwamnati, sun yanke shawarar tsayar da Bello ne saboda shi ne ya zo na biyu a zaben fidda gwani. (Murtala Zhang)