in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Mutane 10 sun mutu a wani harin ta'addanci a arewa maso gabashin kasar
2015-12-13 13:46:49 cri

A kalla mutane goma aka kashe a yayin da aka sace wasu da dama a lokacin da wasu mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari kusa yankin Biu dake jihar Borno, dake arewa maso gabashin Najeriya, in ji majiyoyin wurin.

Musa Tella, wani mazaunin kauyen Kamuya dake wannan yanki, ya bayyana cewa wani gungun mayakan sun kai harin a ranar Alhamis da yamma, tare da harba bindigogi da kuma tilastawa mazauna garin ficewa daga gidajensu.

Mutane goma sha daya suka jikkata, kuma yawancinsu samu raunin harsasai, in ji Musa Tella a wata hira da 'yan jarida. Yawancin gidajen garin an lalata su a lokacin wannan hari. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China