in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nigeriya ya yi jimamin wadanda suka mutu a gobarar matatar iskar gas a kasar
2015-12-26 12:56:42 cri
Shugaban Nigeriya Muhammadu Buhari ya bayyana matuka jimamin shi bisa ga rasa rayukan da wadansu 'yan kasar suka yi a wani gobara da ta tashi a wani matatar iskar gas a garin Nnewi na jihar Anambra dake kudu maso gabashin kasar.

A cikin sanarwar da fadar gwamnati ta fitar a ranar Jumma'a ta bayyana cewa Shugaban Buhari ya kadu matuka kuma ya firgata da adadin mutanen da suka rasa rayukansu a tashin gobara daya.

Shugaban ya mika ta'aziyar shi ga iyalan wadanda suka rasu, al'umma da kuma gwamnatin jihar Anambra bisa abin da ya bayyana da abin bakin cikin da ya faru a wannan lokacin na jajibirin Krismeti.

Ya ce yana mika jajen shi tare da addu'a ga iyalan wadanda suka rasu da yanzu haka suke cikin wani hali na bakin ciki da juyayi.

A kalla mutane 8 ne dai aka tabbatar da mutuwarsu a matatar iskar gas din, kamar yadda kakakin 'yan sandan jihar ta Anambra Ali Okechukwu ya bayyana a ranar Jumm'a. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China