A cikin wata sanarwar da Ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau ya fitar a birnin Ikko, a kuma game da karuwan zanga zanga da ake aiwatarwa a kasar yana mai jaddada cewa demokradiya ta samar da kafofi da al'umma za su bi su isar da korafin su ba tare da tashin hankali ba.
Ministan ya tabbatar da cewar babu wata gwamnati mai iko da za ta nade hannuwan ta , ta bari ana keta doka da zai gurgunta zaman lafiya da cikakken mulkin kasar.
Ya ce a dangane da hakan, ma'aikatar harkokin cikin gida ya ba da umurni ma dukkan hukumomin tsaron karkashin ikon ta da suka hada da 'yan sanda da su tabbatar da cewar sun samar da kariya ga al'ummar kasar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Abdulrahman Dambazau daga nan sai ya yi kira ga al'ummar kasar ta Najeriya da su sa ido sosai tare da ba da rahoton duk wani zirga zirga da ba su yarda da shi ba da kuma mutanen da su ma ba a yarda da su ba ga hukumomin tsaron da ke kusa.(Fatimah Jibril)