Wata sanarwa dauke da sanya hannun kakakin rundunar sojojin Najeriyar kanar Sani Usman ta bayyana cewa, an kubutar da mutanen ne a ranar Litinin a lokacin da sojojin suka kai samame kan wasu sansanonin 'yan ta'addan guda hudu a kusa da Bama, gari na biyu mafi girma a yankin na jihar Borno da mayakan na Boko Haram suka kame a kwanakin baya.
Sanarwar ta kara da cewa, sojojin sun yi nasarar lalata dukkan sansanoni 4 da ke yankin, wadanda suka hada da Faldan,Kidiziromari, da Kuroshini, da Kurumari da kuma Ngulde. Kana an kashe daya daga cikin 'yan tawayen a lokacin da ya ke kokarin arcewa.
Bugu da kari, sojojin sun gano kayayyakin abinci makare a cikin wasu durum-durum, da buhuna da kuma wuraren adana kayayyakin a karkashin kasa.
Sauran kayayyakin da sojojin suna gano a lokacin wannan samame sun hada da kekuna da babura da mayakan na Boko Haram ke amfani da su wajen kai hare-hare kan fararen hula.
Rundunar sojan Najeriyar dai ta ce tana kokarin ganin ta kawo karshen hare-haren masu tayar da kayar bayan a wa'adin wannan wata da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar ya deba musu.(Ibrahim)