Kama shugaban gidan talabijin na AIT dai na zuwa ne a bayan kame Sambo Dasukin da hukumar ta DSS din ta yi domin ya amsa tambayoyi game da dala biliyan biyun da aka ce an yi amfani da su wajen sayen makaman.
A wani labarin kuma, hukumar EFCC ta damke tsohon gwamnan jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya Attahiru Bafarawa dangane da wancan badakalar sayen makaman.
Bugu da kari, hukumar ta EFCC tana farautar tsohon shugaban jam'iyyar PDP Mohammed Haliiru Bello da shi ma ake zargi da karkatar da wasu kudaden sayen makaman.(Ibrahim)