Gwamnatin Nigeriya a ranar talata ta sanar da rage tsarin da take bi na ajiyan ta wanda ake bukatar kashi 25% zuwa kashi 20%, sannan ta rage tsarin ajiyan asusun ta daga kashi 13% zuwa 11%.
Gwamnan babban bankin kasar wato CBN Godwin Emefiele ya sanar da hakan a Abuja bayan taron kwamitin tsarin asusun bankin.
Ya ce, rage adadin kudin wani kokari ne da gwamnati ke yi na inganta tattalin arzikin kasar, sannan kuma wannan tsari zai tabbatar da ganin an saki karin kudade wajen ajiya a bankuna wanda zai habaka ba da rance a bangaren aikin noma da ma'adinai.
A cewar Mr Emefiele, haka kuma wannan tsarin zai inganta samar da sakamako, ya kuma taimaka wajen kara guraben ayyukan yi.(Fatimah Jibril)