in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin yammacin Afirka sun yi kira da a fadada hadin gwiwa
2015-12-17 19:25:38 cri
Shugabannin kasashen yammacin Afirka, sun yi kira da a fadada hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin, ta yadda hakan zai taimakawa dunkulewar su.

Shugabannin sun gabatar da wannan kira ne a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya, yayin taron tattaunawa na shugabannin kungiyar ECOWAS da ya gudana a jiya Laraba.

A jawabin sa na bude taron, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayi kira ga kasashe mambobin kungiyar, da ma sauran shugabannin kasashen duniya, da su hada kai da juna, domin tunkarar matsalar tsaro dake addabar duniya, da ma sauran matsaloli kamar safarar miyagun kwayoyi, da fashin teku, da sauran laifuka da ake aikatawa a kan teku.

A nasa bangare shugaba Macky Sall na kasar Senegal, cewa yayi akwai bukatar hada karfi da karfe, wajen magance matsalar karancin ababen more rayuwa, kamar fannin gine-gine, da na makamashi, da fannin noma, da layin dogo da kuma na wutar lantarki. Shugaba Sall ya ce hakan zai baiwa kasashen yammacin Afirka damar dunkulewa waje guda da cin moriyar juna. Mr. Sall, wanda ke jagorantar kungiyar ECOWAS a wannan lokaci, ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar da su sake duba na tsanaki, su kuma kalubalanci juna, domin cimma nasarar da aka sanya gaba a dukkanin fannoni.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China