Bikin na kwanaki 2 an yi shi ne da nufin taimakama abokai 'yan Nigeriya fahimtar al'adun Sinawa, tarihi, yanayin zaman rayuwa sannan ya inganta musayar al'adu da hadin gwiwwa a nan gaba.
Fiye da mutane 400 ne suka halarci ranar farko na bikin wanda ya hada da jami'an gwammati, malaman makaranta, dalibai da 'yan kasuwa.
A cikin jawabin shi na bude taron, karamin jakadan kasar Sin a Nigeriya, Liu Kan ya ce finafinai na iya saka mutane musayar tunaninsu kuma bikin na da nufin barin mutane kara fahimtar kasar Sin ta hanyar finafinan ta ya kuma fadda bangaren finafinan. (Fatimah)