Shugaban dandalin tattalin arziki na duniya Mista Klaus Schwab, wanda kuma ya kafa wannan dandali, ya halarci babban taro na biyu na yanar gizo ko Intanet dake gudana a garin Wuzhen na lardin Zhejiang na kasar Sin, inda ya shedawa manema labaru cewa, gwagwarmayar masana'antu a mataki na hudu, wadda ke dora muhimmanci matuka kan yanar gizo ko Intanet ta iso ga Bil Adama. A kuma wannan gaba Sin za ta samu bunkasuwa matuka a wannan fanni. Duba da irin ayyukan kirkire-kirkire, da manufar bude kofa da Sin din ke aiwatarwa a wannan fanni.
Mista Schwab ya nuna cewa, a matsayin ta na kasa dake sahun gaba a wannan fanni, Sin ta samu ci gaba mai armashi cikin gwagwarmayar da ake yi a wannan karo.
Ya ce ko da yake tattalin arzikin duniya na fuskantar koma bayan, amma a ganinsa, Sin na samun bunkasuwa mai dorewa yadda ya kamata. (Amina)