in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeriya ta samu fiye da mutane miliyan 48 dake amfani da yanar gizo a ko da yaushe
2014-10-09 10:02:50 cri

Mutane fiye da miliyan 48 aka tabbatar da suna amfani da yanar gizo a ko da yaushe, kamar yadda wata cibiyar raya fasahar sadarwa ta kasar Nageriya NITDA ta sanar da kamfanin dillanci labarai na Xinhua a ranar Laraban nan.

A cikin wata sanarwar da cibiyar ta NITDA ta fitar wadda babban darektanta Peter Jack ya sanya wa hannu, an ce, wannan bangaren na sadarwar ta yanar gizo yana taimaka wa fiye da kashi 8 a cikin 100 na GDPn kasar, kuma yanzu yana karuwa da kashi 7 a cikin 100 a duk shekara.

Cibiyar ta ce, a Nigeriya ana yawan yin ayyuka ta hanyar yanar gizo. Babban burin cibiyar shi ne inganta bangaren sadarwa na zamani wanda a nan gaba zai ba da gudunmuwa ga hauhawar GDPn kasar da kusan kashi 15 a cikin 100 nan da shekaru 3 zuwa 5 masu zuwa.

Sanarwar ta ce, Nigeriya ta inganta wani tsari na sadarwar zamani mai wa'adin shekaru biyar wato daga shekara ta 2010 zuwa 2015, shirya wannan tsari, in ji sanarwar, yana cigaba da tafiya yadda ya kamata a bangarorin ilimi, aikin gona, kiwon lafiya, hukumomin mulki da sashin shari'a.

sauran bangarorin sun hada da cigaban al'umma da tsaron kasa wadanda suka inganta cigaban sashen sadarwar na zamani matuka. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China