Bayan shafe wadannan shekaru yanzu haka al'ummar Sinawa miliyan 632 ne ke amfani da yanar gizo, adadin da ya haura wanda ake da shi a sauran daidaikun kasashen duniya.
Cikin wata budaddiyar wasika da ta fitar a wannan rana, hukumar yanar gizo ta kasar Sin ta ce Sinawa na amfani da yanar gizo a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da na yada al'adu. Sauran fannonin da yanar gizon ke bada gudummawa sun hada da kiwon lafiya da kuma Ilimi. A cewar hukumar kamata ya yi jama'a su kara kulawa, wajen amfani da wannan kafa ta hanyar da ta dace.
A ranar 14 ga watan Satumbar shekarar 1987 ne dai wani dakin gwajin fasahar sadarwa dake nan birnin Beijing, ya aike da sakon email na farko zuwa ga wata jami'a dake kasar Jamus, sakon dake cewa "tun daga nan Babbar ganuwa, muna iya isa dukkanin sassan duniya".