in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bayyana matukar damuwa da hari kan na'urorinta masu kwakwalwa da Amurka ke yi
2013-06-24 09:42:50 cri

Kasar Sin ta bayyana matukar damuwa da yadda gwamnatin Amurka ke kaiwa na'urorinta masu kwakwalwa hari, kamar dai yadda wasu rahotanni daga kafofin yada labaru suka tabbatar da wannan zargi.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Madam Hua Chunying ce ta bayyana hakan, yayin da take amsa tambayoyin manema labarai don gane da harin da wasu kafofin watsa labaru suka yi zargin Amurkan ta kai, kan wasu na'urorin kamfanonin wayar sadarwa, da kuma na jami'ar Tsinghua dake nan kasar Sin. Hua ta ce, wannan batu ya tabbatar da zargin da Sin din ke yi wa Amurka, kuma tuni aka fara daukar matakan da suka wajaba domin shawo kan lamarin.

Har ila yau, Hua ta kara nanata rashin amincewar kasar Sin ga dukkanin wani yunkuri na kai hari kan na'urori masu kwakwalwa a ko ina su ke, ta kuma jaddada aniyar mahukuntan kasar Sin na hawa teburin shawarwari, da hadin gwiwa, da martaba juna tsakaninta da ragowar kasashen duniya, duka dai da nufin wanzar da dauwamamman yanayin zaman lafiya, da tsaron na'urori masu kwakwalwa da kasashe ke amfani da su. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China