in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kamfanonin yanar gizo na Sin karo na 7 a Washington
2014-12-03 13:27:57 cri

A ranar Talata 2 ga watan nan ne aka bude taron kamfanonin yanar gizo na kasar Sin karo na 7 a birnin Washington na kasar Amurka. Taron da ya samu halartar wakilan gwamnatoci sama da 150, da wakilan masana'antu, da masana daga sassan duniya daban daban.

Ana dai sa ran tattauna batutuwan da suka jibanci hadin gwiwar masu ruwa da tsaki na kasashen Sin da Amurka a fannin tsaron yanar gizo. Musamman a wannan gaba da sassan biyu ke fuskantar kalubale na rashin amicewa juna a wasu harkokin da suka jibanci amfani da kafar ta yanar gizo.

A jawabinsa yayin taron minista mai kula da harkokin yanar gizo na kasar Sin Lu Wei, ya ce, Internet ta zamo muhimmiyar kafa ta samar da ci gaban sassan biyu, don haka akwai bukatar inganta alaka tare da daukar matakan hadin giwar sassan biyu a wannan fanni.

Mr. Lu ya kara da cewa, bai kamata banbance-banbance dake tsakani ya haifar da tarnaki ba. A ganinsa kamata ya yi wadannan sabane-sabane su bude kafofin ci gaban hadin kai da cimma moriyar juna.

Ita kuwa wakiliyar kasar Amurka Catherine Novelli, cewa ta yi ya dace kasar ta da kasar Sin su hada karfi waje guda, domin cin moriyar ribar dake kunshe a harkar ta'ammali da yanar gizo. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China