in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta dakatar da aikin hadin gwiwar tsaron yanar gizo da Amurka
2014-05-20 10:08:33 cri

Kasar Sin ta bayyana dakatar da hadin gwiwar da take yi da kasar Amurka a fannin tsaron yanar gizo. Hakan dai a cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya biyo bayan zargin da Amurkan ta yiwa wasu jami'an sojin Sin su 5, na leken asirin wasu kamfanonin Amurka ta yanar gizo.

A jiya Litinin ne dai ma'aikatar shari'ar Amurka ta bayyana zargin da ake wa jami'an sojin na kasar Sin, ko da yake mahukuntan kasar ta Sin sun yi watsi da zargin suna masu cewa, ba shi da tushe bare makama.

Da yake karin haske game da wannan zargi, da kuma matakin da Sin ta dauka, Mr. Qin ya ce, wajibi ne Amurka ta janye wannan zargi maras tushe, domin kuwa rashin yin hakan na iya gurgunta kyakkyawar huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Kaza lika Mr. Qin Gang ya ce, matsayin kasar Sin game da satar bayanai ta yanar gizo a bayyane yake, wato dai ko kadan Sin ba ta da aniyar satar bayanan wata kasa. Hasali ma dai Amurka ce aka sha jin kafofin yada labaru na kasa da kasa, na zargin ta da aikata wannan laifi na satar bayanai ta hanyoyi da dama.

Mr. Qin ya kara da cewa, kasarsa za ta dauki karin matakai game da wannan batu, gwargwadon yadda al'amura suka wakana. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China