Dangane da hakan, Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a ranar 25 ga wata a nan Beijing cewa, hukumar Hong Kong ta daidaita batun bisa dokoki, lamarin da babu wanda zai iya nuna shakku ko zargi a kai, kuma kamata ya yi bangarori daban daban masu ruwa da tsaki su mutunta hakan. Shakkar da Amurka ta nuna wa Hong Kong game da gudanar da ayyuka bisa dokoki ba ta da ma'ana, sa'an nan kuma, gwamnatin kasar Sin ba ta amince da zargin da Amurka ta yi mata ba, saboda ba ta da isassun shaidu.
Game da batun tsaron yanar gizo ta Internet kuwa, madam Hua ta ce, kasar Sin ta ba ta lamunci duk wani harin da aka kai wa yanar gizo ba, haka kuma ta ki yarda da tsara ma'auni iri 2 kan wannan batu. Don haka kasar Sin tana fatan kasashen duniya za su tattauna da yin hadin gwiwa cikin himma, daidaita matsalolin tsaron Internet yadda ya kamata, da kiyaye zaman lafiya da tsaron kai a Internet tare, bisa ruhun girmama juna da amincewa da juna.
Har wa yau kuma, dangane da furucin da Amurka ta yi na cewa, batun Edward Snowden zai kawo illa ga huldar da ke tsakanin Sin da Amurka, madam Hua ta ce, kasar Sin tana fatan Amurka da ita za su aiwatar da muhimmin ra'ayi daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma a tsanake, za su inganta tattaunawa da hadin gwiwa a tsakaninsu, da daidaita sabani yadda ya kamata, a kokarin raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 zuwa sabon mataki. (Tasallah)