in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin a MDD ya yi kiran da a kiyaye tsaron yanar gizo a duniya
2015-07-02 11:08:30 cri

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana a jiya Laraba cewa, tsaron yanar gizo ya zama muhimmin batun dake da nasaba da 'yancin mulkin kasa da tsaro da kuma harkokin bunkasuwa na kasashe daban daban na duniya.

Don haka, ya kamata kasashen duniya su kiyaye tsaron yanar gizo ta hanyar yin musayar ra'ayi da hadin gwiwa bisa tushen girmama juna da zaman daidaito gami da kawo moriyar juna cikin adalci.

Mr. Liu Jieyi ya bayyana hakan ne a gun taron farko na tattaunawa kan yadda ake aiwatar da sakamakon da aka samu a gun taron koli na sadarwa na duniya. Inda ya kara da cewa, ya kamata kasashen duniya su dauki matakan da suka dace domin tinkarar ayyukan da kungiyar 'yan ta'adda suka yi ta yanar gizo wajen wallafa hotunan bidiyo da yada tsattsauran ra'ayi da horas da 'yan ta'adda da tattara kudade da tsara shirin ta'addanci da kuma gudanar da ayyukan ta'addanci.

A cewarsa, kasar Sin ta yi kira da a tsara yarjejeniyar yaki da laifufukan da ake aikatawa ta yanar gizo ta kasa da kasa bisa jagorancin MDD, kuma ta yi kira ga kasashe daban daban da su nuna himma da kwazo wajen sa hannu cikin ayyukan kungiyar kwararru masu yaki da laifuffukan yanar gizo ta MDD.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China