in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin da ke kula da bayanai na yanar gizo na kasar Sin ya ce, Amurka ta saci bayanai daga yanar gizo na kasar Sin
2014-05-20 14:43:33 cri

Ma'aikatar shari'a ta kasar Amurka ta sanar da kai karar jami'an sojoji 5 na kasar Sin bisa laifin satar bayanai ta intanet a ranar litinin 19 ga wata. Sakamakon haka ofishin da ke kula da bayanai na intanet na kasar Sin ya fitar da cikakken bayanai da ke nuna yadda Amurka ta saci bayanan yanar gizon kasar Sin, inda aka nuna cewa, Amurka ita ce ta fi satar asiri a intanet a duk duniya, wadda kuma ta zama babbar kasa ta farko da ke kai hari kan yanar gizon kasar Sin.

Bayanin ya yi nuni da cewa, daga ranar 19 ga watan Maris zuwa ranar 18 ga watan Mayu na bana, manyan na'urorin sarrafa bayanai masu kwakwalwa na Amurka da yawansu ya kai 2077 sun sarrafa na'urori masu kwakwalwa na kasar Sin miliyan 1.18 kai tsaye. Ban da wannan kuma, kwamfotoci 135 na kasar Amurkan sun sarrafa shafunan intanet 563, wadanda aka tsara don leken arisin kasar Sin, wannan haka ya zamo keta iko ne kimanin dubu 14, laifuffukan sun hada da kafa tashar intanet na jabu, da satar bayanai daga jama'a masu zaman kansu, da kuma satar lambar sirri ta jama'a. wasu daga cikinsu ma sun saci sirrin kasuwanci, yayin kuma wasu suka aikata zamba, abin da ya kawo babbar hasara ga jama'ar kasar Sin. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China