in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta habaka bangaren samar da kayayyakin sadarwar internet ga Tanzaniya
2014-11-20 10:22:29 cri

Zuba jarin da kasar Sin ta yi a Tanzaniya ya ba da wata damar habaka bangaren sadarwar internet ga kasar, in ji ministan sadarwar, kimiyya da fasasha na kasar Makame M. Mbarawa jiya Laraba.

Ministan da ya ke bayyana hakan lokacin babban taro na duniya a kan internet a garin Wuzhen dake jihar Zhejiang a gabashin kasar Sin ya ce, da taimakon kamfanonin sadarwa na kasar Sin, al'ummar Tanzaniya da dama yanzu suna da kafar sadarwar Internet, kuma wannan bangaren ya samu gaggarumin ci gaba a cikin shekarun da suka biyo baya ta wajen amfani da shi a wayar salulan su don tafiyar da ayyukan yau da kullum da suka hada da biyan kudaden kai tsaye ta yanar gizon.

Ya ce, kamfanin da ya ba da taimakon haka kuwa shi ne kamfanin gina kayayyakin sadarwar kasa da kasa na kasar Sin wato "China International Communication Construction Company" wadda ta zama kashin bayan duk wani salon sadarwar yanar gizo a kasar ta Tanzaniya.

Minista Makame ya ce, wannan kamfanin ya hada manyan birane na Tanzaniya har ma ya taimaka wajen samar da igiyoyin wayar sadarwa na karkashin ruwa ga sauran kasashe makwabta a gabashi da kudancin Afrika kamar Burundi, Malawi da Uganda. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China