Na farko shi ne kara inganta tsarin samun bayani WB(Wide Band) da kafa sabon dandalin bunkasa tsarin WB. Na biyu shi ne kara fadada yin amfani da internet a fannonin masana'antu, aikin gona, hada-hadar kudi, ciniki, bada ilmi, kiwon lafiya da dai sauransu, da sa kaimi ga neman bunkasuwa a harkar shiga internet da sauran harkokin yau da kullum. Sai na uku wanda shi ne kara tabbatar da ikon mallakar fasaha, da kafa wani irin tsarin kirkiro da kamfanoni da za su jagoranci harkar internet ta yadda gwamnati za ta sa kaimi, da bangarori daban daban su zuba jari da kuma cin moriya tare. (Zainab)