in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta zama babbar kasuwa da ta fi girma a duk duniya kan sayar da kayayyaki ta yanar gizo
2014-03-11 16:35:44 cri

Mataimakin darektan ofishin kula da harkokin kasuwanci ta yanar gizo na ma'aikatar kasuwancin Sin Mista Zhang Peidong ya bayyana cewa, kididdigar da aka bayar, ya nuna cewa, yawan cinikin da aka yi ta yanar gizo a Sin a shekarar 2013 ya zarce kudin Sin Yuan biliyan dubu 10.

A zantawarsa da manema labarai a ran lahadi 9 ga wata, Mr Zhang yayi bayanin cewa daga cikinsu darajar kayayyakin da aka sayar ga jama'a ta kai Yuan biliyan 1850, sakamakon haka ne, kasar Sin ta zama babbar kasuwa da ta fi girma a duk duniya kan sana'ar sayar da kayayyaki ga jama'a ta yanar gizo. Ya kara da cewa kasuwanci ta yanar gizo yana kawo babban tasiri ga zaman rayuwar al'umma, a cikin shekaru 5 da suka gabata, yawan kudin cinikayyarsa ya ninka sau biyu, matsakaicin karuwar cinikin kayayyaki da aka sayar ga jama'a ta karu da kashi 80 bisa dari a ko wace shekara.

A 'yan shekarun baya, sha'anin aika sako cikin gaggawa ya karu cikin sauri, wanda saurinsa ya wuce tunanin jama'a. A shekara ta 2006, yawan sakonnin da a kan aika ta wannan hanya ya kai biliyan guda, amma a shekarar 2013, yawan su ya kai biliyan 9.2, kashi 60 daga cikinsu an yi oda ne daga yanar gizo.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China