An bude taron sauyin yanayi a cibiyar Le Bourget Exhibition dake birnin Paris, da sanyin safiyar litinin din nan. Shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping na cikin shugabanni mahalarta bikin bude taron.
Shugabanni daga kasashe fiye da 150 sun halallara domin gabatar da shawarwari kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris tare da nuna goyon bayan su a siyasance. Shugaba Xi zai gabatar da jawabi a gun bikin, inda zai bayyana matsayi da ra'ayoyin Sin game da kyautata yanayin duniya.
Bisa ajandar taron, bayan bikin bude taron shugabanni mahalarta taron za su baiwa wakilansu izinin shiga shawarwari kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, don kafa wani tsari wanda zai dace da dukkanin kasashe masu sa hannu game da tinkarar kalubalen sauyin yanayi bayan shekarar 2020. (Amina)