Yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya jaddada bukatar kasashen biyu, da su ci gaba da gina dangantaka mai inganci, karkashin manufofin kaucewa tada hankali da rashin jituwa, tare da hada gwiwa wajen tabbatar da cimma moriyar juna.
Har ila yau shugaba Xi ya yi nuni ga muhimmancin ci gaba da hadin kan kasashen Sin da Amurka, a fannin al'amuran da suka shafi kasa da kasa da na shiyya shiyya, kamar tsara manufofin bunkasa tattalin arziki, da cimma nasara a wannan taro na MDD game da sauyin yanayi, tare kuma da cimma daidaito a fannonin da ake da sabani a kan su, cikin kyakkyawan yanayi.