A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da ke halartar kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 23 da ke gudana a birnin Manila da ke kasar Phillipines, ya mayar da martani game da kisan wani Basine da kungiyar IS ta yi.
Shugaban Xi ya ce, da kakkausan murya kasar Sin ta yi Allah-wadai da kisan Basinen da kungiyar IS ta yi, ya kuma mika jaje ga iyalin mamacin. Ya kara da cewa, ayyukan ta'addanci ya zama abokan gaban bil-Adama, kuma kasar Sin tana adawa ga duk wani nau'i na ayyukan ta'addanci, sannan za ta yi yaki da duk ayyukan ta'addanci da ake kaiwa kan bil- Adama.
A wannan rana, firaministan Sin Li Keqiang ya nuna Allah-wadai da wannan aika-aikar da kungiyar IS ta yi, kuma ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da inganta tsaron Sinawa a kasashen waje.(Bako)