in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya bayyana tunanin kasar kan shirya taron koli na G20 a shekara mai zuwa
2015-11-17 09:07:57 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi karin bayani kan yadda kasar Sin za ta shirya taron kolin G20 karo na 11 daga ranar 4 zuwa 5 ga watan Satumbar shekarar 2016, yayin jawabin da ya gabatar a taron kolin kungiyar G20 da ke gudana a birnin Antalya na kasar Turkiya.

Bisa halin da ake ciki yanzu da kuma burin da sassa daban daban suke neman cimmawa, kasar Sin na kokarin maida "bunkasa tattalin arzikin duniya ta hanyar kirkire-kirkire, wadda ke da karfin yin cudanya da juna" a matsayin babban taken taron.

Har ila kasar Sin za ta shirya tarukan share fage a fannoni 4, wato sabunta hanyar bunkasuwa, kyautata yadda ake kula da tattalin arziki da harkokin kudi a duniya, kara azama kan harkokin cinikayya da zuba jari a duniya, sa kaimi kan samun ci gaba ta hanyar yin cudanya da juna.

Dangane da batun yin gyare-gyare a asusun ba da lamuni na duniya, shugaba Xi ya jaddada cewa, makasudin yin kwaskwarima ga asusun shi ne kara wakilcin kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa da kasashe masu tasowa da kuma 'yancinsu na bayyana ra'ayoyi. Kasar Sin na maraba da shawarar da asusun ya gabatar a kwanan baya, dangane da sanya kudin kasar Sin na RMB cikin kudaden ajiya na ketare.

Dangane da batun yaki da cin hanci da karbar rashawa kuwa, shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan yaki da cin hanci da karbar rashawa, da kuma gurfanar da dukkan wadanda suka aikata laifin a gaban kotu, kuma kasar Sin ba za ta kawar da kai ga wannan laifin ba.

Ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta inganta yin hadin gwiwa da kasashen duniya a wannan fanni. Har wa yau, kasar Sin na goyon bayan kungiyar G20 wajen kyautata yin hadin gwiwa a fannonin damke wadanda suka aikata wannan laifi tare da maido da kudaden da suka sata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China