in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gabatar da sakon taya murnar ranar goyon bayan Palesdinawa
2015-11-24 13:59:43 cri
A jiya Litinin 23 ga watan nan ne MDD ta gudanar da taron ranar nuna goyon baya ga Palesdinawa, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya buga waya ga mahalarta taron yana mai nuna farin cikin sa da gudanar taron.

Xi Jinping ya bayyana cewa, warware matsalar Palesdinu daga dukkan fannoni cikin adalci, ya dace da moriyar jama'ar Palesdinu da ma ta sauran kasashen dake yankin, kana zai sa kaimi ga samun zaman lafiya da lumana a duniya. Ya ce kamata ya yi a warware matsalar Palesdinu ta hanyar gudanar da shawarwari cikin lumana.

Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin tana goyon bayan shiga-tsakani wajen shimfida yanayin zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila. Kaza lika kasar na fatan ci gaba da kokari tare da kasa da kasa, wajen cimma burin samun zaman lafiya mai dorewa a dukkan fannoni a yankin gabas ta tsakiya kuma cikin hanzari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China