Cikin wani bayanin da jaridar "The Herald" ta kasar Zimbabwe ta wallafa, shugaban na Sin ya ce bunkasa hadin gwiwa da Zimbabwe, da ma sauran kasashen Afirka, na daya daga cikin muhimman manufofin diflomasiyyar kasar ta Sin, duk kuwa da sauye sauyen da ake fuskanta a fagen dangantakar kasashen duniya.
Shugaba Xi ya kara da cewa, Sin za ta yi aiki kafada da kafada da Zimbabwe, da ma sauran kawayen ta na nahiyar Afirka, wajen fadada hanyoyin cimma moriyar juna, da ci gaba tsakanin Sin da kasashen Afirka.
Wannan tsokaci na shugaba Xi na zuwa ne gabanin ziyayar aiki ta yini biyu da zai gudanar a Zimbabwe, a ranekun Talata da Laraba, bisa gayyatar shugaba Robert Mugabe.