Huang Ping ya yi nuni da cewa, kasashen Sin da Zimbabwe sun taimaka da juna yayin da suke raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummarsu, kana an samu nasarori kan hadin gwiwar da ke tsakaninsu. Kasar Sin tana daukar kasar Zimbabwe a matsayin abokiyar cinikayya ta biyu kana kasa ta farko a bangaren zuba jari, kuma hukumomin hada-hadar kudi na kasar Sin sun tattara kudi tare da zuba jari ga kamfanonin Sin don su gudanar da manyan ayyukan fadada ayyukan more rayuwa a kasar Zimbabwe kamar filin jiragen sama na Victoria Falls da tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa da ke kudancin gabar tebkin Kariba da dai sauransu. A yayin ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Zimbabwe, kasashen biyu za su daddale wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwa kan ayyukan more rayuwa. Bayan kammala wadannan manyan ayyuka, ana fatan za a kawo karshen matsalolin rashin wutar lantarki, da sufuri da dai sauransu, kuma hakan zai taimaka wajen raya tattalin arzikin kasar ta Zimbabwe. (Zainab)