Xi Jinping ya nuna cewa, bayan da annobar cutar Ebola ta barke a wasu kasashen yammacin Afirka, nan da nan kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwa ta kasar sun tsai da kudurin tallafawa kasashen Afirka wadanda suke fama da cutar bisa namijin kokarinta na kara sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Afirka. Wannan ya alamta cewa, kasar Sin babbar kasa ce dake kokarin sauke nauyin da ke kanta, kuma ta bayar da muhimmiyar gudummawarta wajen karfafa da kuma bunkasa zumuncin dake kasancewa tsakanin kasashen Sin da Afirka.
Bugu da kari, shugaba Xi Jinping yana fatan hukumomin gwamnatoci na matakai daban daban da na soja za su ba da muhimmanci ga batun tabbatar da lafiyar jama'a, kana su dauki kwararan matakai na yin rigakafi da shawo kan duk wata annoba cikin lokaci, ta yadda za a tabbatar da ganin cewa kasar Sin ta zama kasar da al'ummominta suke zaune cikin koshin lafiya, kuma za su iya bayar da gudummawarsu wajen cimma burin bunkasuwar kasar Sin baki daya. (Sanusi Chen)