in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya isa birnin Manila don halartar taron APEC
2015-11-17 15:21:22 cri

A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Manila hedkwatar kasar Philippines, don halartar taron koli na kwarya-kwarya karo na 23 na kungiyar hadin gwiwa kan tattalin arziki na yankunan Asiya da tekun Fasific wato APEC.

Taken taron na wannan karo shi ne, "Raya tattalin arziki daga duk fannoni, don gina kyakkyawar duniyar da muke ciki", shugabannin kasashe mambobin kungiyar APEC da ke halartar taron, za su tattauna batutuwan da suka shafi dunkulewar tattalin arzikin yankin waje daya, da raya matsakaita da kananan masana'antu da horar da kwararru da samun dauwamammen ci gaba da dai sauransu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China