in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Faransa
2015-11-30 09:50:51 cri

A jiya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Faransa François Hollande a birnin Paris.

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, ya kamata manyan jami'an gwamnatocin kasashen biyu su ci gaba da yin shawarwari a fannin siyasa tare da tattauna muhimman ayyukan hadin gwiwa da daddale muhimmiyar yarjejeniyar hadin gwiwa tsakaninsu. Ya ce, ya zama wajibi a tashi tsaye don karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci a matakai daban daban na kasashen biyu da kara mu'amala ta fuskokin tattalin arziki da cinikayya, al'adu, kimiyya da fasaha, ilmi, da yawon shakatawa da dai sauransu, don kyautata dangantakar al'ummomin kasashen biyu. Shugaba Xi ya jinjina kokarin da Faransa ta yi na shirya babban taro game da batun sauyin yanayi da zai gudana a birnin Paris,

A nasa bangare, shugaba Hollande ya ce, ya kamata bangarorin biyu su gudanar da hakikanin hadin gwiwa kamar yadda shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito a kai, don karfafa hadin gwiwa a fannonin saka jari, tattalin arziki da cinikayya, da makamashin nukiliya da dai makamantansu, don sa kaimi ga mu'amalar jama'ar kasashen biyu. Ya ce, kasar Faransa tana goyon bayan taron kolin G20 da Sin za ta shirya a shekara mai zuwa, kuma tana fatan inganta hadin gwiwa da kasar Sin game da manyan batutuwan duniya da na shiyya-shiyya.

Shugaban Hollande ya ci gaba da bayyana cewa, yana maraba da shugaba Xi na halartar babban taron sauyin yanayi na Paris, matakin da ya nuna tsayayyiyar anniyar Sin na ganin an cimma wata yarjejeniya a karshen taron.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China