in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali don warware matsalar 'yan gudun hijira
2015-11-21 16:01:21 cri

Zaunannen walilin kasar Sin dake MDD Mista Liu Jieyi ya bayyana a ranar jumma'a 20 ga wata cewa, matsalar 'yan gudun hijira da ta bullo a yankin Bahar Rum ya sami asali ne saboda rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali da kasa samun bunkasuwa cikin daidaito, don haka ya kamata a dauki mataki na neman samun zaman lafiya da bunkasuwa don warware wannan matsala baki daya.

Babban taron majalisar ta kira wani cikakken taro game da matsalar 'yan gudun hijira a yankin Bahar Rum, inda Mista Liu ya yi jawabi cewa, yake-yake da tashin hankali muhimman dalilai ne da suka haifar da matsalar 'yan gudun hijira da kaurar mutane. Hanya daya kawai da za a bi don warware wannan batu shi ne samun bunkasuwa cikin lumana ta yadda jama'ar kasashe masu tasowa za su iya yin zaman rayuwa cikin jituwa da tabbatar hakkinsu.

Ban da wannan kuma, Mista Liu ya yi kira da a nace ga manufar daukan nauyi dake wuyan kasashe daban-daban da kara hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa ta fuskar 'yan gudun hijira. Mista Liu kuma ya kara da cewa, tun barkewar rikicin kasar Sham, Sin ta baiwa jama'ar kasar Sham da 'yan gudun hijira dake kasashe daban-daban tallafinta ta hanyoyi daban-daban da kimarsa ta kai fiye da kudin Sin miliyan 230. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China