in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya yi tsokaci game da halartar shugaba Xi Jinping taron G20 da na APEC
2015-11-19 20:37:53 cri
Daga ranar 14 zuwa 19 ga watan nan, bisa goron gayyatar da ya samu, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron koli karo na 10 na kungiyar G20 a birnin Antalyar kasar Turkiyya, da kwarya kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 23 da aka gudanar a birnin Manila na Philippines.

A yayin kammala ziyarar ta shugaba Xi, ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya zanta da manema labarai game da ziyarar, inda ya bayyana cewa ziyarar ta sami babbar nasara. Ya ce cikin kwanaki 6 da suka wuce, shugaba Xi ya halarci ayyuka sama da 10 a wadannan tarukan koli guda biyu, tare da gabatar da jawabai masu muhimmanci.

Kaza lika shugaban kasar ta Sin ya kuma halarci kwarya kwaryar taron shugabannin kungiyar BRICS, tare kuma da ganawa da shugabanni da kusoshin kasa da kasa sama da 10.

Shugaba Xi ya bayyana ra'ayin kasar Sin game da muhimman batuttuwan duniya a fannonin tattalin arziki da siyasa, matakin da ya ba da jagoranci ga hadin gwiwa na shiyya shiyya a yankin Asiya da tekun Pasifik. Kuma ya bayyana sabon yanayi da ra'ayin Sin na neman samun bunkasuwa, tare da kara samun fahimta, amincewa, da kuma taimakawa juna tsakanin mambobin kungiyar kasashen na yankin Asiya da tekun Pasifik. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China