in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya kai ziyara a kasar Malaysia
2015-11-20 13:39:18 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya tashi daga nan birnin Beijing domin kai ziyara a birnin Kuala Lumpur hedkwatar kasar Malaysia, tare da halartar jerin tarurruka 3.

A cikin kwanaki 3 masu zuwa, firaministan Sin zai halarci taron koli karo na 18 na kasar Sin da kasashen kudu maso gabashin Asiya Asean da taron koli karo na 18 na kasashen Sin, Japan da Koriya ta Kudu da kungiyar Asean da kuma taron kolin kasashen dake yankin Gabashin Asiya karo na 10. Sannan kuma, zai kai ziyara a hukunce a kasar Malaysia. Masana sun nuna cewa, a lokacin da ake samun hadin gwiwar yankin gabashin Asiya, ziyarar firaministan Sin na wannan karo zai kawo kuzari ga aikin dunkulewar kasashen da ke yankin gabashin Asiya baki daya, gami da raya hadin gwiwar dake yankin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China