in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi suka game da hallaka wasu 'yan kasarta 3 da aka yi garkuwa da su a otel din Mali
2015-11-21 12:53:13 cri

Kasar Sin ta yi alawadai da harin da masu dauke da makamai na Al-Murabitoun suka kai a otel din Radison Blu dake birnin Bamako na kasar Mali wanda ya kawo asaran rayukan mutane 27, ciki har da 'yan kasarta 3.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Hong Lei ya sanar da hakan a safiyar Asabar din nan a nan birnin Beijing, yana mai bayanin cewa Sin ta mai da hankali sosai game da wannan lamari sannan ma'aikatar harkokin wajenta da ofiishin jakadancinta dake kasar Mali sun riga sun kaddamar da shirin ba da agajin gaggawa da aikin ceto.

Gwamnatin kasar Mali da sauran kasashen duniya sun yi iyakacin kokarinsu wajen ba da ceto amma duk da hakan 'yan kungiyar suka nuna rashin tausaya ma ran dan Adam ta hanyar aiwatar da mummunan ayyukansu.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Mr Hong ya tabbatar da cewa, an ceto 4 daga cikin Sinawan dake cikin otel din a lokacin da aka kai harin. Gwamnatin kasar Sin tana mika matukar juyayinta tare da mika ta'aziya ga iyalan wadanda wannan harin ya rutsa da su.
Ya ce Sin za ta ci gaba da aiki tare da sauran kasashen duniya domin tabbatar da ingantaccen kariya da kare hakki na al'ummar Sinawa da hukumominsu dake kasashen waje.

 

Ban da wannan kuma, babban magatakardan MDD Mista Ban Ki-Moon ya yi Allah wadai da harin da aka kai a wani Otel din kasar Mali. A cikin sanarwar tasa, ya jajanta tare da mika ta'azziya ga gwamnatin Mali saboda rasa rayukan wadannan mutane cikin harin. Ya ce, an kai hari a wannan karo a daidai lokacin gudanar da aikin shimfidar zaman lafiya a Mali, da kakkausar murya ya yi tir da duk wani mataki da aka dauka wanda ya karya "yarjejeniyar shimfidar zaman lafiya da sulhuntawa", kuma a cewarsa, majalisar tana goyon bayan duk wani matakin da Mali za ta dauka na tinkarar ta'addanci.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China