Wang Yi ya kara da cewa, wadannan Sinawa injiniyoyi uku wadanda aka hallaka su sun ziyarci kasar Mali ne domin taimakawa neman ci gaban kasashen Afirka da kawo alheri ga 'yan Afirka. Ana bakin ciki kwarai game da rasuwarsu, sakamakon haka, ya ce gwamnati na mika ta'aziyyarta ga iyalan wadannan mutane.
Har ila yau ya ce kasar Sin na da imani cewa, dukkan jama'ar kasashen Afirka su ma su yi suka da kakkausar murya da kuma kyamar irin wannan mummunan matakin ta'addanci maras tausayi.
Ministan harkokin wajen Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan matsayin yakar ta'addanci da ake yi ta kowace hanya kuma a kowane wuri, sannan tana ganin cewa, ya kamata gamayyar kasa da kasa ta dauki kwararan matakai na yin hadin gwiwa domin yakar ta'addanci yadda ya kamata. (Sanusi Chen)