Mataimakin shugaban hukumar koli ta ayyukan sojin kasar Sin Fan Changlong, ya ce kasar sa za ta zurfafa hadin gwiwa da kasar Mali a fannin ayyukan soji.
Mr. Fan wanda ya bayyana hakan yayin zantawar sa da ministan tsaron kasar Mali Tieman Coulibaly jiya Alhamis a nan birnin Beijing, ya kara da cewa Sin da Mali kawaye ne na kut da kut, kana Sin na daukar Mali a matsayin aminiya a nahiyar Afirka, wadda kuma ta dade tana hadin gwiwa da Sin a harkokin da suka shafi kasa da kasa.
Ya ce Sin na da burin kara taka rawar da ta dace a bangaren wanzar da zaman lafiya da lumana a Mali.
A nasa bangare Coulibaly, godewa mahukuntan kasar Sin ya yi bisa tallafi da suke baiwa Mali a tsahon lokaci, yana mai fatan bangarorin biyu za su kara azama wajen fadada hadin gwiwarsu a fannin ayyukan soji, ciki hadda ayyukan wanzar da zaman lafiya da kuma horas da jami'ai.(Saminu Alhassan)