Liu Jieyi ya ce, kamata ya yi MDD ta kara saurin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya, da kara saurin kafa tare da jibge rundunar sojan kiyaye zaman lafiya, da kyautata aikin ba da guzuri, domin amfani da albarkatun kiyaye zaman lafiya yadda ya kamata. Ban da haka, kamata ya yi MDD ta kara horar da ma'aikatan kiyaye zaman lafiya, da kara sa ido kansu, domin gudanar da ayyukan cikin yanayi mai kyau.
Dadin dadawa, mista Liu ya kara da cewa, a matsayin zaunanniyar memba ta kwamitin sulhu na MDD, da kasa mai tasowa mafi girma a duniya, Sin tana tsayawa tsayin daka kan goyon baya ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, kuma ta kebe kudi da tura sojoji da yawa sakamakon haka. Sin ta riga ta sanar da shiga sabon tsarin shiryawa kan ayyukan kiyaye zaman lafiya da MDD ta kafa, kuma za ta tura karin sojojin injiniyoyi, da na jigila, da na likitoci da sauransu. (Fatima Liu)