in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci jagoran ayarin jiragen ruwan yakin Amurka da ke tekun Fasific da ya ja kunnen sojojinsa
2015-11-20 10:34:57 cri
A yammacin jiya ne mamban a kwamitin kula da harkokin soji na kwamitin tsakiya na JKS kuma kwamandan sojojin ruwa na Sin Wu Shengli ya gana da janar Scott Swift jagoran ayarin jiragen ruwan yakin Amurka da ke tekun Fasific da ke ziyara a nan birnin Beijing.

Mr. Wu ya maraba da zuwan tawagar ayarin jiragen ruwan yaki karkashin shugabancin Janar Swift, inda ya jaddada cewa, a cikin 'yan shekarun nan, sojojin ruwan kasashen biyu sun kara mu'amala gami da karfafa hakikanin hadin gwiwa a tsakaninsu, amma kwanan baya, bangaren Amurka ya tura jiragen ruwan yaki zuwa tsibiran dake kusa da yankunan tekun kudancin Sin da sunan 'yancin zirga-zirga, abun da ya kawo babbar barazana game da ikon mulkin kan kasar Sin.

Sojojin Sin sun yi sintiri gami da yin kashedi da dama game da aika-aikar da Amurka ta yi, kuma Sin ta kai zuciyar nesa bisa tunanin kiyaye dangantakar kasashen biyu. Amma idan Amurka ta rufe idanunta game da adawar kasar Sin, sannan ta ci gaba da yi mata barazana,to Sin tana da karfi wajen kiyaye 'yanci da tsaronta.

Wu Shengli ya ce, ya kamata sojojin ruwan kasashen Sin da Amurka su martaba alkawuran da shugabannin kasashen biyu suka cimma, don yalwata da karfafa hakikanin hadin gwiwa da mu'amala a tsakaninsu, ta yadda za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da kuma shiyya-shiyya.

A nasa jawabin, janar Swift ya ce, an raya dangantakar sojojin ruwa na kasashen biyu cikin armashi, kana suna hadin gwiwa yadda ya kamata, sojojin ruwan Amurka ba su fatan batun kudancin tekun kasar Sin ya lalata dangantakar da ke tsakanin sojojin ruwa na kasashen biyu, yana fatan bangarorin biyu za su ci gaba da inganta mu'amala da kara yin atisayen sojin ruwa tsakanin bangarorin biyu, don magance duk wani kuskure da rashin fahimtar juna, har ma da abin da ka iya biyo baya a tsakaninsu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China